13 Yuni 2025 - 05:14
Source: ABNA24
Isra'ila Tana Luguden Hare-Hare A Iran

Anji karar fashe-fashe da dama a Tehran da kuma harba makaman kariya a Tehran/Hare-Haren ta'addanci mafi girma a tarihin kasar Iran. An kai hari kan hedikwatar dakarun kare juyin juya halin Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbayt (As) - ABNA - ya habarta cewa: Tashar talabijin ta Times of Israel ta bayar da rahoton cewa, ta nakalto ministan tsaron Isra'ila Katz cewa, an kafa dokar ta-baci a dukkan yankunan da ta mamaye sakamakon ayyukan da Isra'ila ke yi a Iran.

Cibiyoyin sadarwa sun tabbatar da labarin da ake jin kararraki a Tehran. Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya sanar da cewa: Sojojin saman gwamnatin kasar sun kai wani hari ta sama kan kasar Iran.

A karo da dama, ana iya jin karar harbe-harbe ta sama a Tehran inda Tehran ke karkabo makaman da Isra'ila ta harbo zuwa gareta.

Isra'ila ta kai hari kan na'urar tsaron saman Teheran don yuwuwar cigaban hare-haren mai girma da za ta fara daga baya!

Rundunar ta IDF ta sanar da fara wani sabon farmakin soji mai suna "Jajircewar Zaki" kan shirin nukiliyar Iran da kuma karfin makamai masu linzami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A karon farko na farmakin an kai hare-hare da dama kan sansanonin soji a yankuna daban-daban na Iran.

A cewar sanarwar, hare-haren da aka kaiwa Iran sun hada da:

Cibiyoyin bada umarnin soja

Wuraren kwamandojin

Sansanonin soja da kayayyakin more rayuwa

Kutse cikin shafukan da ke da alaƙa da shirin nukiliya.

Anji Kararrawar gargadin da aka a duk fadin yankunan da aka mamaye ba don harba makami mai linzami ba ne, a'a don shiryar da jama'a ta hanyar kowa yayi ta kansa don tunani game da yiwuwar kai harin makami mai linzami daga Iran.

Baya ga wuraren da sojoji suka kai harin, an nufi wasu kwamandojin sojojin Iran ne.

Har yanzu ana jin karar jiragen da ke kaiwa da komowa a wasu sassan Tehran

Abubuwan Da Suke Faruwa: 

Jaridar Hume ta Isra'ila: Isra'ila na neman kai hari kan manyan jami'an soji a Tehran. Akwai yara da dama daga cikin shahidan harin na daren yau...

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa filin jirgin Imam Khumaini

Ofishin Hulda da jama'a na filin jirgin Imam: Babu wani abu da ya faru da filin jirgin Imam a yanzu. Har sai Hukumar Kula da Jiragen Sama ta bayyana mana halin da ake ciki, a halin yanzu mun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama don ganin yadda lamarin zai kaya.

Kamfanin dillancin labaran ya tabbatar da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan Natanz, Khorramabad, da Hamedan.

Zuwa haɗa wannan rahoton Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren Isra'ila a wurare daban-daban da suka hada da Arak, Karaj, Natanz da...

Ministan tsaron Isra'ila:

Mun kai ga matsayin da ba komowa ko ja da baya;

An fara yakin tashin tashina tsakanin Iran da Isra'ila.

Gwamnatin Sahayoniya: An fara kai wa Iran hari zagaye na uku. Fashe-fashe da dama a cibiyoyin nukiliyar Iran.

Allah Ta'ala Ya Taimaki Iran Da Karfinsa Da Ikonsa Albarkar Imam Ali As

Your Comment

You are replying to: .
captcha